Kamfanin dillancin labaran Ikna ya nakalto daga jaridar (Jakarta Post) cewa; ministan mai kula da harkokin addini a kasar Indonesia ya yi kira ga 'yan siya da su guji yin amfani da alkur'ani mai tsarki wajen cimma manufofinsu na kamfen siyasa a kasar. Ministan ya ci gaba da cewa kur'ani littafi ne mai tsarki na addini, wanda bai kamata wasu 'yan siyasa su mayar da ayoyin da ke cikinsa wata hanya ta yin kamfen siyasa ba domin kawai mutane su zabe su a matsayin masu kishin addini, ya ce ko kadan hakan ba daidai ba ne, ya ce ya kamata ne 'yan siyasa su yi amfani da kafofin yada labaransu, da hakan ya hada da mujallu jaridu da dai sauransu, tare da bayyana ma mutane gaskiya dangane da manufofinsu, ba sai sun fake da kur'ani ba wajen gamsar da mutane.
Kasar Indonesia dai kasa ce da ke yawan musulmi, inda adadin musulmin kasar ya kai kashi 90% a cikin adadin mutanen kasar da ya kai miliyan 230, kuma za a gudanar da zabukan 'yan majalisar kasar a kasa da makonni biyu masu zuwa.
380754