Cibiyar da ke kula da harkokin kur'ani a Iran Ikna ce bayan ta nakalto daga majiyar labarai ta Nasij ta bada labarin cewa; wannan taro za a kwashe kwanaki uku ana gudanar da shi karkashin kulawar sarkin kasar muhammadu na shidda kuma akwai halartar wakilai daga kasashen Masar ,Hadaddiyar daular larabawa ,Mauritaniya, Saudiya da Koweiti. Wannan shi ne karo na biyu da kasar ke shirya irin wannan taro da zummar habaka sha'anin addini da kara kusanta al'umma da harkokin addini da ruhi na addini musamman a tsakanin matasa .
381331