Daga jamhuriyar Karkizistan ne cibiyar da ke kula da harkokin kur'ani a Iran Ikna ta watsa rahoton cewa: za a fara koyar da mata karatun kur'ani a fadar mulkin kasar karkizistan da cibiyar musulunci ta Sadap ta dauki dawainiyar hakan.Jami'ar musuluncii a birnin ne ya ware guri a falfajiyarta domin bawa mata wannan dama ta daukan darasin karatun kur'ani sau hudu a mako inda za a rika koyar da su karatu da tajwidi daga malummansu mata.
383732