Bangaren kasa da kasa: Wakilan kasashen musulmi da na larabawa sun fice daga zauren taron majalisun dokoki na kasashen duniya da aka gudanar a kasar Ethiopia, domin nuna rashin amincewarsu da siyasar danniya da mamayar Isra'ila kan al'ummar palastinu, bayan da wani dan majalisar Isra'ila ya fara bude taron da jawabi.
Kamfanin dillancin labaran Ikna ya nakalto daga kamfanin dillancin labaran (SABA) cewa; a wani mataki na nuna goyon baya ga al'ummar palastinu, wakilan kasashen musulmi da na larabawa sun fice daga zauren taron majalisun dokoki na kasashen duniya da aka gudanar a kasar Ethiopia, domin nuna rashin amincewarsu da siyasar danniya da mamayar Isra'ila kan al'ummar palastinu, bayan da wani dan majalisar Isra'ila ya fara bude taron da jawabi. Rahoton ya kara da cewa wakilan kasar Yeman da suke halartar taron ne suka fara ficewa bayan da wakilin Haramtacciyar Kasar Isra'ila ya fara jawabi a gaban taron, daga nan kuma sai sauran wakilan kasashen musulmi da na larabawa da suke halartar taron duk suka fice baki daya, bayan da ya kammala kuma sai suka dawo. An kafa majialisar hadin kan majalisun dokoki na kasashen duniya karkashin kulawar majalisar dinkin duniya a cikin shekara ta 1989, kuma wannan shi ne karo na dari da ashirin da take gudanar da babban taronta.
385729