Kamfanin dillancin labaran ikna ya nakalto daga shafin internet na kamfanin dillancin labaran (mohit) cewa; mahalarta taro birnin Istanbul na kasar Turkiya da aka gudanar kan ayyukan kur'ani mai tsarki, sun bukaci a kafa wani kwamitin mahardata kur'ani a kasashen gabacin turai. Rahoton ya ce shugabannin cibiyoyin da ke kula da ayyukan kur'ani a kasashen musulmi da na larabawa, gami da wasu kasashen gabacin nahiyar turai da ma wasu kasashen gabacin Asia, sun cimma matsaya kan bukatar da aka gabatar wa gaban taron, da ke neman a kafa wani babban kwamiti, da zai kula ayyukan kur'ani a gabacin nahiyar turai. Mahalarta taron sun jaddada cewa wajibi ne a mayar da hankali wajen koyar da 'yan musulmi musamman yara kanana karatun kur'ani mai tsarki.
385643