Bangaren kasa da kasa: A ranar juma'ar da ta gabata jami'an tsaron Haramtacciyar Kasar Isra'ila sun dauki kwararan matakan tsaro, da nufin hana gudanar da sallar juma'a, inda ta hana daruruwan palastinawa shiga cikin harabar masallacin tun daga jijjifin safiyar ranar juma'a, inda suka bar tsoffi kawai suka shiga cikin masallacin domin gudanar da sallar.
Kamfanin dillancin labaran ikan ya nakalto daga kamfanin dillancin labaran kasar Kuwat (Kuta) cewa; a ranar juma'ar da ta gabata jami'an tsaron Haramtacciyar Kasar Isra'ila sun dauki kwararan matakan tsaro, da nufin hana gudanar da sallar juma'a, inda ta hana daruruwan palastinawa shiga cikin harabar masallacin tun daga jijjifin safiyar ranar juma'a, inda suka bar tsoffi kawai suka shiga cikin masallacin domin gudanar da sallar. Rahoton ya kara da cewa jami'an tsaron Haramtacciyar Kasar Isra'ila a cikin kayan sarki sun yi ta binciken katin shedar zama dan kasa na palastinawa, kafin su bari su shiga cikin masallacin Qods, inda sukan hana mutanen da shekarunsu ke kasa da arba'in, tare da korarsu daga yankin da masallacin yake ko da kuwa sun nuna katin shedar zama dan kasa. Rahoton ya ce ga alama Isra'ila na shirin daukar matakan hana gudanar da sallar juma'a ne a cikin masallacin Qods mai alfarma a nan gaba.
386096