IQNA

Za A Gudanar Da Taro Kan Hakkokin Mata A Musulunci A Yamen

16:33 - April 20, 2009
Lambar Labari: 1767583
Bangaren kasa da kasa: Za a gudanar da taro kan hakkokin mata a mahangar musulunci a birnin Baida da ke kudancin birnin San'a fadar mulkin kasar Yamen.
Kamfanin dillancin Ikna ya nakalto daga kamfanin dillancin labaran sabanews cewa; za a gudanar da taro kan hakkokin mata a mahangar musulunci a birnin Baida da ke kudancin birnin San'a fadar mulkin kasar Yamen. Rahoton ya ci gaba da cewa taron na yini guda zai tabo muhimman batutuwa dangane da hakkokin mata da kuma yin dubi kan mahangar muusulunci a kansu. Jami'ar Darbaida ce ta shirya gudanar da taron, wanda zai samu halartar wasu daga cikin malaman addini na kasar, gami dam asana daga jami'oin kasar, inda za su gabatar da jawabai, tare da makaloli kan mahangar musulunci dangane da hakkokin mace. Babbar manufar gudanar da taron dai kamar yadda shugaban jami'ar ya fada shi ne wayar da kan magidanta dangane da hakkokin mata ya yadda ya kamata su kiyaye ka'idojin musulunci a rayuwa ta zamantakewa.

390857



captcha