Kamfanin dillancin labaran Ikna ya nakalto daga kamfanin dillancin labaran kasar Saudiyya SPA cewa; za a gudanar da wani taro na kasa da kasa domin nuna kayayyakin tarihin musulunci daga kasashen musulmi daban-daban a birnin Riyad fadar mulkin kasar saudiyya. Shugaban kwamitin kula daharkokin yawan shkatawa na kasar Saudiyya Salman Bin Abdulaziz ya bayyana cewa gwamnatin Saudiyya tana iyakacin kokarinta domin tattara kayayyakin tarihin musulunci na kasar, domin nuna su a wajen taron. Kayyakin da za a nuna wajen taron sun hada da muhimman abubuwan tarihin musulunci na tsawon shekaru da suka gabata, yanzu haka an ware wani wuri na musamman domin tara irin wadannan kayayyaki.
393971