Kamfanin dillancin labaran Ikna ya nakalto daga jaridar Alqods da ake bugawa a kasar Kuwait cewa; cibiyar kula da al'adun muslunci a kasar Belgium za ta gudanar da gasar hardar kur'ani a birnin Brussel da aka baiwa suna gasar sarkin Kuwat. Bayanin ya ci gaba da cewa babbar manufar gudanar da wannan gasa dai ita ce karfafa musulmin kasar Belgium marassa rinjaye wajen karatun kur'ani da kuma hardarsa. Ofishin jakadancin kasar Kuwait ne zai dauki nauyin sa ido dangane da yadda gasar za ta gudana. Wadda za ta samu halartar mutane da dama daga sassa daban-daban na kasar. Za a gudanar da gasar ne a bangarorin harda da kuma karatu, sai kuma bangaren tajwidi, wato sanin ka'idojin karatun kur'ani.
393852