Kamfanin dillancin labaran Ikna ya habarta cewa, a cikin hudubar Juma'a da limamin juma'a na birnin Mashahad ya gabatar a wannan makon, ya bayyana cewa mun yi imani da fadar kur'ani cewa gushewar karya da tabbatar gaskiya lamari ne da babu shakku a cikinsa, saboda haka wannan hukunci bai kebance Amurka ba. Ya ci gaba da cewa zaluncin da Amurka take aikatawa kan al'ummomin musuli a kasashen Afganistan da Iraki da kuma labanan gami da palastinu ba mai dorewa ba ne, kuma barazanar da Amurka ke yi kan jamhuriyar Musulunci ta Iran bat a da wani tasiri, domin kuwa Iran kasa ce da ta dogara da Allah, barazanar mahluki ba za ta iya tsorata ta ba.
393907