IQNA

Za A Gudanar Da Gasar Hardar Kur'ani A Wales

13:56 - April 27, 2009
Lambar Labari: 1770570
Bnagaren kasa da kasa: Cibiyar da ke kula harkokin musulmi a Wales ta arewa za ta gudanar da gasar hardar kur'ani a cikin watan Mayu mai kamawa.
Kamfanin dillancin labaran Ikna yan nakalto daga shafin internet na NWIS cewa: cibiyar da ke kula harkokin musulmi a Wales ta arewa za ta gudanar da gasar hardar kur'ani a cikin watan Mayu mai kamawa. Za a gudanar da gasar ne a babban masallacin birnin Yinagor na Wales ta arewa. Bayanin ya ci gaba da cewa wadanda za su shiga gasar za su kara da juna net a bangaren harda da kuma tajwidi, kuma bangaren hardar za a fi mayar da hankali ne a cikin surorin bakara da kuma ali imran, inda za a kula da harda da kuma tajwidi wato sanin ka'idojin karatun kur'ani. Za a bayar da kyaututtuka ga wadanda suka zo na daya da na biyu da na uku a kowane bangare.

394583














captcha