IQNA

Za A Gudanar Da Taro Kan Tattalin Arzikin Kasashen Musulmi

14:05 - April 27, 2009
Lambar Labari: 1770575
Bangaren kasa da kasa: Babban sakataren kungiyar hadin kan kasashen musulmi ta OIC Akmaluddin Auglo ya bayyana cewa zai halarci taron da za a gudanar a kasar Malazia kan harkokin tattalin arzikin kasashen musulmi.
Kamfanin dillancin labaran Ikna ya habarta cewa; Babban sakataren kungiyar hadin kan kasashen musulmi ta OIC Akmaluddin Auglo ya bayyana cewa zai halarci taron da za a gudanar a kasar Malazia kan harkokin tattalin arzikin kasashen musulmi. Auglo ya ce taron wanda za a gudanar a jami'ar IIUM da ke birnin Kualalampour fadar mulkin kasar Malazia, zai yi dubi ne kan matsalolin tattalin arziki da suka addabi duniya, da kuma tattauna hanyoyin day a kamata gwamnatocin kasashen musulmi su bi wajen kaucewa fadawa cikin matasalar, ko kuma rage kaifinta ta yadda ba za ta yi tasiri cikin harkokin tattalin arzikinsu ba. Ya ce zai halarci taron kuma zai gabatar da jawabi dangane da wadannan matsaloli tare da bayar da shawarwarin da suka dace ga kasashen musulmi.

394621
captcha