Kamfanin dillancin labaran Ikna ya habarta cewa; kakakin ma'aikatar shari'a a kasar Iran Abbas Ali Kodkhodai, ya bayyana cewa; wasu daga cikin manyan kasashen duniya suna yin amfani da batun kare hakkin dan adam ne wajen cimma manufofinsu na siyasa domin ci gaba da danne sauran al'ummomi masu rauni. Ya bayyana hakan ne a lokacin da yake gabatar da wani jawabi a gaban taron da wasu masana kan harkokin shari'a suka shirya gudanarwa a babban dakin taro na jami'ar Tehran. Ya ce batun kare hakkin dan adam batu ne na 'yan adamtaka wasu lokuta kuma yan adangantaka da shari'a, amma abin ban takaici kasashe masu girman kai sun mayar da hakan ya zama batu na siyasa, domin kawai ta hakan ne za su iya cimma wasu bakaken manufofin na su.
395516