Bangaren siyasa da zamantakewa: Dole ne musulmi su farga dangane da tarkon da makiya suke haka musu na rarrabar kanunsu, kuma ya kamata ne soyayyar iyalan gidan manzo (AS) ta zama wani abin da zai hada kan al'ummar musulmi.
Kamfanin dillancin labaran Ikna ya habarta cewa; a cikin wani jawabi da ya gabatar a gaban wani taro da aka gudanar a garin mahsha da ke kasar Iran, shugaban cibiyar kula da ayyukan yada addinin musulunci reshen mahsha Abbasi ya bayyana cewa; dole ne musulmi su farga dangane da tarkon da makiya suke haka musu na rarrabar kanunsu, kuma ya kamata ne soyayyar iyalan gidan manzo (AS) ta zama wani abin da zai hada kan al'ummar musulmi. Ya ci gaba da cewa soyayyar iyalan gidan manzon Allah wani wajibi ne a kan dukkanin musulmi, amma makiya musulunci suna son su yi amfani da hakan wajen rudar wasu daga cikin musulmi domin kawo rarraba a cikin wannan al'umma. Ya ce son iyalan gidan manzo da kuma yin koyi da su ita ce sahihiyar hanya ta yin koyi da manzon Allah day a kamata duk musulmi su yi riko da ita.
395397