Bangaren kasa da kasa; Cibiyoyin yada ilimi da al'adun musulunci na kasashen musulmi suna da karancin mutane masu cikakkiyar masaniya kan al'adun turai, ta yadda za su iya isar da sakon muslunci kamar yadda ya kamata, wannan ya sanya masu isar da sakon suna fuskantar matsaloli da dama a wadannan kasashe.
Kamfanin dillancin labaran Ikna ya nakalto daga jaridar sharq ausat cewa; malamin jami'a na birnin Oslo fadar mulkin kasar Norway Lina Larsen ya bayyana cewa; cibiyoyin yada ilimi da al'adun musulunci na kasashen musulmi suna da karancin mutane masu cikakkiyar masaniya kan al'adun turai, ta yadda za su iya isar da sakon muslunci kamar yadda ya kamata, wannan ya sanya masu isar da sakon suna fuskantar matsaloli da dama a wadannan kasashe. Lina Larsen ya bayyana hakan ne a lokacin da yake zantawa da shugaban kungiyar musulmi ta kasar, ya ci gaba da cewa a hakikanin gaskiya al'ummomin kasashen turai ba su da masaniya kan addinin musulunci, day a kamata kasashen musulmi su rika bayar da horo ga mutanen da suka san al'adun turai a rika tura su domin wayar da kan mutanen nahiyar dangane da manufofin addinin musulunci.
396113