IQNA

An Kafa Asusun Kula Da Ayyukan Muslunci A Afirka Ta Kudu

13:36 - April 29, 2009
Lambar Labari: 1771681
Bangaren kasa da kasa: An kafa wani asusu domin gudanar da ayyukan muslunci a jiya a kasar Afirka ta kudu.
Kamfanin dillancin labarann Ikna ya nakalto daga jaridar sharq alawsat cewa; wannan asusu an kafa shi ne a kasuwar hannayen jari ta birnin Johannesburg, a bangaren da ake saye da sayar da hannayen jari. Bayanin ya ci gaba da cewa kimanin iyalai 400 ne na muslmi da suke gudanar da harkokinsu a bangaren saka hannayen jari suka bude wannan asusu, inda suka fara saka kudade da nufin taimaka ma dukkanin harkokin addinin musulunci da ake gudanarwa a kasar. Yanzu haka dai asusun yana da tsabar kudi rand miliyan 27, wanda kuma kowane rand na kasar Afirka ta kudu yana kwatankwacin dala takwas ne, kuma tuni aka kafa kwamiti wanda za a dorawa alhakin kula da asusun da kuma sarrafa kudin da ke cikinsa ta hanyar da ta dace.

396080



captcha