Bangaren kasa da kasa: Ministan mai kula da harkokin addini na kasar Syria Mohammad Abdulsattar sayyid a wajen taron ministocin ma'aikatun kula da harkokin addini na kasashen musulmi ya kirayi dukkanin kasashen musulmi da su yi aiki tare da juna domin cimma manufofinsu a matsayinsu na kasashen musulmi.
Kamfanin dillancin labaran Ikna ya nakalto daga kamfanin dillancin labaran kasar Syria SANA cewa; Ministan mai kula da harkokin addini na kasar Syria Mohammad Abdulsattar sayyid a wajen taron ministocin ma'aikatun kula da harkokin addini na kasashen musulmi ya kirayi dukkanin kasashen musulmi da su yi aiki tare da juna domin cimma manufofinsu a matsayinsu na kasashen musulmi. Ya bayyana hakan ne a taron da ministocin kula da harkokin addinin na kasashen musulmi suka gudanar a birnin Jidda na kasar Saudiyya, wanda kuma wannan shi ne karo na biyar da aka gudanar da irin wannan taro. Ya ci gaba da cewa babban abin da kasashen musulmi suke bukata a halin yanzu shi ne yin aiki kafada da kafada domin cimma burinsu, tare da shawo kan duk wani tsattsauran ra'ayi da wuce gona da iri da sunan addini.
411341