Bangaren kasa da kasa: Daraktan cibiyar wayar da kai dangane da halin da marassa rinjaye suke ciki a Saudiyya Abdulaziz Bin Abdullah ya bayyana cewa, an bude wani dakin karatu na musulunci da yake dauke da littafai na turanci a yankin Alkasim na kasar Saudiyya.
Kamfanin dillancin labaran Ikna ya nakalto daga jaridar Aljazira da ake bugawa a kasar Saudiyya cewa; Daraktan cibiyar wayar da kai dangane da halin da marassa rinjaye suke ciki a Saudiyya Abdulaziz Bin Abdullah ya bayyana cewa, an bude wani dakin karatu na musulunci da yake dauke da littafai na turanci a yankin Alkasim na kasar Saudiyya. Ya ci gaba da cewa wannan katafaren dakin karatu ya kunshi littafai da aka tarjama a cikin harshen turanci, ko kuma aka rubuta su a cikin harshen, wadanda suka shafi bangarorin tarihin musulunci, da sirar manzon Allah SAW gami da littafan fikihu da na hadisi, da dai sauran bangarori na addinin musulunci, wanda hakan zai taimaka ma wadanda suke fahimtar harshen turancin ingilishi fahimtar wasu abubuwa na addini da aka rubuta ko tarjama a cikin harshen turanci.
412772