IQNA

Musulmi Na Neman Shugabancin Majalisar Dokokin Jahar Virginia Ta Amurka

12:20 - June 01, 2009
Lambar Labari: 1785499
Bangaren kasa da kasa: Shugaban kwamitin kula da harkokin musulmi na kasar Amurka ya bayyana cewa a shirye yake ya nemi shugabancin majalisar dokokin jahar Virginia, bayan da aka zabe shi a matsayin dan majalisar dokokin jahar.
Kamfanin dillancin labaran Ikna ya nakalto daga shafin internet na Aljazeera cewa; Shugaban kwamitin kula da harkokin musulmi na kasar Amurka ya bayyana cewa a shirye yake ya nemi shugabancin majalisar dokokin jahar Virginia, bayan da aka zabe shi a matsayin dan majalisar dokokin jahar. A cikin bayanin da shugaban kwamitin kula da harkokin musulmin na kasar Amurka ya fitar ya bayyana cewa; mabiya addinin musulunci na fuskantar matsaloli da dama a mafi yawan yankunan Amurka, daga ciki kuwa har da jahar Virginia, y ace idan dai har ya samu damar zama shugaban majalisar dokoki na jahar, to zai iyakacin kokarinsa wajen ganin an shawo kan matsaloli da dama da musulmi suke fuskanta a jahar, daga ciki kuwa har da nunua musu banbanci da wariya da kyamata daga saura al'ummomin jahar wadanda ba musulmi ba.

413165

captcha