Kamfanin dillancin labaran Ikna ya nakalto daga kamfanin dillancin labaran wam na hadaddiyar daular larabawa cewa; babban sakataren kwamitin kula da ayyukan kare masallacin Qods da ya hada da mabiya addinin musulunci da kuma mabiya addinin kirista Hassan Khatir ya bayyana cewa; Manyan malaman yahudawa suna yin amfani da littafin Attaura wajen kara karfafa gwiwar shugabannin Isra'ila domin ci gaba da aikata laifukan wuce gona da iri a yankunan palastinawa da kuma birnin Qods mai alfarma. Hassan Khatir ya bayyana hakan ne a cikin wani bayani day a fitar a jiya dangane da halin da masallacin Qods da sauran wurare masu tsarki da ke birnin suke ciki, inda yahudawan sahyuniya ke yi barazanar rusa su domin kowa ya rasa.
413683