IQNA

Za A Bude Wata Cibiyar Koyar Da Kur'ani Ga Kananan Yara A Madina

23:33 - July 03, 2009
Lambar Labari: 1797692
Bangaren kasa da kasa; Za a bude wata cibiyar koyar da karatun kur'ani mai tsarki ga kananan yara a birnin Madina mai alfarma, wanda kwamitin kula da harkokin mata na birnin Madina ya dauki nauyin budewa da kuma gudanar da dukkanin shirye-shiryen cibiyar, wanda za a fara nan bad a jimawa ba.
Kamfanin dillancin labaran Ikna ya nakalto daga kamfanin dillancin labaran was na kasar saudiyya cewa; Za a bude wata cibiyar koyar da karatun kur'ani mai tsarki ga kananan yara a birnin Madina mai alfarma, wanda kwamitin kula da harkokin mata na birnin Madina ya dauki nauyin budewa da kuma gudanar da dukkanin shirye-shiryen cibiyar, wanda za a fara nan bad a jimawa ba. Shugaban bangaren da ke kula da harkokin kur'ani na kwamitin ya bayyana cewa , bude wannan cibiyar zai taimaka matuka wajen koyar da kananan yara karatun kur'ani mai tsarki da kuma haradarsa gami da ilimin tajawidi, wanda hakan zai bayar da dama ga yaea su san kur'ani yadda ya kamata.

428137



captcha