IQNA

An Girmama Mahardata Kur'ani Mata Da Ke Fadin Kasar Kuwait

23:32 - July 03, 2009
Lambar Labari: 1797696
Bangaren kasa da kasa; A jiya ne aka gudanar da wani gagarumin biki na girmama mata mahardata kur'ani mai tsarki a kasar Kuwait, wanda cibiyar kula da harkokin mata ta kasar ta dauki nauyin shiryawa da gudanarwa a fadin kasar.
Kamfanin dillancin labaran Ikna ya nakalto daga jaridar Alkabs ta kasar Kuwait cewa; A jiya ne aka gudanar da wani gagarumin biki na girmama mata mahardata kur'ani mai tsarki a kasar Kuwait, wanda cibiyar kula da harkokin mata ta kasar ta dauki nauyin shiryawa da gudanarwa a fadin kasar. Bayanin ya ci gaba da cewa cibiyar kula da harkokin mata ta kasar ta shirya wannan taron ne da nufin kara karfafa gwiwar mata makaranta kur'ani da kuma mahrdata, domin su kara bada himma wajen ci gaba da gudanar da ayyukansua fagen kur'ani mai tsarki, ta yadda za su iya bayar da ta su gudunmawa wajen tarbiyantar da al'ummar musulmi bisa tarbiya ta kur'ani maitsarki. Haka nan kuma hakan zai kara jawo hankulan sauran mata da matasa zuwa ga kur'ani, wanda hakan ko shakka babu zai taimaka matuka wajen gyara tarbiyarsu.

428308







captcha