Bangaren siyasa da zamantakewa; Iraniyawa mazauna kasar Malazia suna gudanar da maulidin Imam Ali (AS) daga ranakun 14 ga watan Tir har zuwa 18 ga watan Tir, wanda cibiyar kula da harkokin addinin musulunci da al'adu ta kasar reshen kasar Malazia ta shirya gudanarwa a birnin Kualalampur fadar mulkin kasar.
Kamfanin dillancin labaran Ikna ya nakalto daga bangaren kula da hulda da jama'a na cibiyar kula da harkokin addinin musulunci da aladu ta Iran reshen kasar Malazia cewa; Iraniyawa mazauna kasar Malazia suna gudanar da maulidin Imam Ali (AS) daga ranakun 14 ga watan Tir har zuwa 18 ga watan Tir, wanda cibiyar kula da harkokin addinin musulunci da al'adu ta kasar reshen kasar Malazia ta shirya gudanarwa a birnin Kualalampur fadar mulkin kasar. Bayanin ya ci gaba da cewa taron yana samun halartar mutanen kasar Malazia musamman ma mabiya mazhabar shi'a daga cikinsu, ana gudanar da taron ne a husainiyar Salman Farsi da ke birnin Kualalampur.
429802