IQNA

An Gudanar Da wani Taro Kan Rawar Da Iran Ke Takawa A Duniyar Musulmi

23:13 - July 06, 2009
Lambar Labari: 1798952
Bangaren kasa da kasa; An gudanar da wani taro day a yi dubi kan irin rawar da jamhuriyar musulunci ta Iran take takawa a bangarori daban-daban na ilmantarwa a duniyar musulmi a jami'ar Lavrov ta kasar Birtaniya, wanda bangaren kula da harkokin al'adu na Iran ya dauki nauyin shiryawa.
Kamfanin dillancin labaran Ikna ya habarta cewa; An gudanar da wani taro day a yi dubi kan irin rawar da jamhuriyar musulunci ta Iran take takawa a bangarori daban-daban na ilmantarwa a duniyar musulmi a jami'ar Lavrov ta kasar Birtaniya, wanda bangaren kula da harkokin al'adu na Iran ya dauki nauyin shiryawa. Bayanin ya ci gaba da cewa taron ya samu halartar wasu daga cikin malaman jami'ar da kuma dalibai da dama, da suka hada da dalibai Iraniyawa da suke karatu a jami'oin kasar Birtaniya, inda wasu daga cikinsu suka baje kolin kayan al'adu da ilimi da fusaha na Iraniyawa, da kuma hotunan wuraren shakatawa da ke kasar Iran.

429824




captcha