Bangaren kasa da kasa; Za a bude wata cibiyar nazarin addinin musulunci a kasar Newzerland a shekara mai zuwa, wanda kuma wannan shi ne karon farko da za a bude wata cibiyar musulunci kasar, da nufin bayar da dama ga masu bincike a jami'oin kasar kan addinin musulunci su samu wurin gudanar da bincike cikin sauki.
Kamfanin dillancin labaran Ikna ya nakalto daga shafin internet na ODT cewa; Za a bude wata cibiyar nazarin addinin musulunci a kasar Newzerland a shekara mai zuwa, wanda kuma wannan shi ne karon farko da za a bude wata cibiyar musulunci kasar, da nufin bayar da dama ga masu bincike a jami'oin kasar kan addinin musulunci su samu wurin gudanar da bincike cikin sauki. Bayanin ya ci gaba da cewa shugabannin jami'oin Otaco da kuma Victoria na kasar ne suka bullo da wannan shiri, wanda zai taimaka ma dalibansu da ke gudanar da bincike kan addinin musulunci su samu madora, musamman ma dangane da abin da ya shafi bangaren siyasar addinin musulunci da kuma bangaren al'adu da zamantakewa da kuma mazhaba.
430502