Bangaren kasa da kasa; An fara gudanar da wani zaman taro dangane da rawar da kafofin yada labarai na kasashen larabawa za su iya takawa musamman ma gidajen radiyo da talabijin, wajen kare martabar birnin Qods, wanda cibiyar kula harkokin radiyo da talabijin na kasashen larabawa ta shirya gudanarwa a kasar Tunisia.
Kamfanin dillancin labaran Ikna ya nakalto daga kamfanin dillancin labaran infotunisie cewa; An fara gudanar da wani zaman taro dangane da rawar da kafofin yada labarai na kasashen larabawa za su iya takawa musamman ma gidajen radiyo da talabijin, wajen kare martabar birnin Qods, wanda cibiyar kula harkokin radiyo da talabijin na kasashen larabawa ta shirya gudanarwa a kasar Tunisia. Bayanin ya ci gaba da cewa An fara gudanar da zaman taron net un ranar Asabar da ta gabata, taron yana samun halartar masana kan harkokin sadarwa da yada labarai daga kasashen larabawa daban-daban, inda suke yin bahasi dangane da irin rawar da dukkanin kafofin yada labarai na kasashen larabawa na yankin gabas ta tsakiya na arewacin Afirka za su iya takawa wajen kare martabar birnin Qods da kuma masallaci mai alfarma.
432588