Bangaren kasa da kasa; Yaduwar akidar kiyayya da musulmi da kuma addinin musulunci na ta kara yaduwa a cikin kasashen da ke nahiyar turai, lamarin da ke ta kara jefa musulmin da ke cikin nahiyar a cikin wani mawuyacin hali.
Kamfanin dillancin labaran Ikna ya nakalto daga cibiyar CECLR cewa; babban daraktan da ke kula da cibiyar yaki da nuna bangaranci da nuna wariyar launin fata na kasar Belgium ya bayyana cewa; Yaduwar akidar kiyayya da musulmi da kuma addinin musulunci na ta kara yaduwa a cikin kasashen da ke nahiyar turai, lamarin da ke ta kara jefa musulmin da ke cikin nahiyar a cikin wani mawuyacin hali. Bayanin ya ci gaba da cewa akwai mutanen da suke da akida ta kiyayya da musulunci, wanda kuma hakan yana tattare da bababn hadari, domin kiyayya da wani addini ko wata jama'a saboda akidarsu ta addini da suka yi imani da ita ya yi hannun riga da kyawawan dabi'u da kare da kare hakkin dan adam da al'ummomin turai suka nuna wa duniya.
432510