IQNA

An Fara Samun Saukin Kyamatar Musulmi A Cikin nahiyar Turai

15:09 - August 02, 2009
Lambar Labari: 1807159
Bangaren kasa da kasa; An fara samun saukin kyamatar mabiya addinin musulunci a cikin wasu kasashe na nahiyar turai kamar yadda wani jin ra'ayin jama'a ya nuna wanda cibiyar bincike ta Club ta gudanar.
Kamfanin dillancin labaran Ikan ya nakalto daga kamfanin dillancin labaran Habar cewa; jaridar Observer ta kasar Birtaniya ta buga wani rahoto da ke cewa; An fara samun saukin kyamatar mabiya addinin musulunci a cikin wasu kasashe na nahiyar turai kamar yadda wani jin ra'ayin jama'a ya nuna wanda cibiyar bincike ta Club ta gudanar. Bayanin ya ci gaba da cewa idan aka kwatanta da lokutan baya inda da dama daga cikin al'ummomin nahiyar turai suka dauki tsananin gaba da addinin muslunci sakamakon siyasar da wasu kasashe suka dauka ta bayyana addinin musulunci a matsayin addinin tashin hankali, yanzu hakan ya ragu matuka a kasashe da daman a nahiyar.

439474


captcha