Kamfanin dillancin labaran Ikna ya nakalto daga kamfanin dillancin labaran Karachai cewa; Wasu daga cikin yara mausulmi 'yan makarantar sakandare a kasar Rasha, za su isa kasar Turkiya domin samun horo kan ilmomin addinin addinin musulunci da kuma karatun kur'ani, bayan haka kuma za su koyi hanyoyin yin nazari kan muhimman abubuwa da suka danganci addinin musulunci. Bayanin ya ci gaba da cewa wannan wani bangare ne na wata yarjejeniya da aka kulla tsakanin Turkiya da kuma babbar cibiyar addinin musulunci ta kasar Rasha, inda ma'aikatar kula da harkokin addinin musulunci ta kasar Turkiya ita ce za ta kula da aiwatar da wannan yarjejeniya.
440676