Kamfanin dillancin labaran Ikna ya nakalto daga shafin interner na kamfanin dillancin labaran Dunya Bulteni cewa; Gwamnatin kasar Girka ta bayar da umurnin rushe wani masallaci mai tsohon tarihi a yankin Yenece da ke yammaci kasar. Bayanin ya ci gaba da cewa tarihin wannan masallaci yana komawa zuwa ga daruruwan shekaru, bayan da daular usmaniya ta gina shi, kuma yanzu haka daruruwan musulmi mazauna yankin suna gudanar da harkokinsu na addini a cikin wannan masalalci, da hakan ya hada da salla, da taruka na addini, amma duk da haka tuni gwamnatin kasar Girka ta bayar da umurnin a rushe shi, wanda kuma a kowane lokaci za a iya rushe shi.
441548