Kamfanin dillancin labaran Ikna ya nakalto daga shafin internet na cibiyar muslumin kasar Amurka reshen birnin Hustan cewa; Za a gudanar da tarukan maulidin Imam Mahdi AS a birnin Hustan na jahar Texas a kasar Amurka, domin gabatar da bayanai dangane da matsayin Imamul hujja da kuma hikimar fakuwarsa da irin yadda ake amfanuwa da fakuwarsa. Bayanin ya ci gaba da cewa wannan na daya daga cikin irin taruka da musulmi musamman ma mabiya mazhabar shi'a suke gabatarwa a kasar Amurka, ba wai kawai a jahar Texas har ma da sauran jahohin kasar inda ked a mabiya addinin musulunci.
441491