Kamfanin dillancin labaran Ikna ya nakalto daga bangaren yada labarai na cibiyar yada al'adu da danganataka tsakanin kasashen musulmi ta kasar Iran cewa; Cibiyoyin ilimi na biranan Qom da Najaf suna taka gagarumar rawa wajen yada ilmomin kur'ani mai tsarki ta hanyoyi da dama, duk da cewa suna yada ilmomin na hukunce-hukuncen addini dad a hadisi da usul gami da ilmin akida wato tauhi da dai sauransu, amma gishikin dukkanin wadannan ilmomi da cibiyoyin suke bayarwa ya ginu ne a kan kur'ani mai tsarki. Bayanin ya ci gaba da cewa wadannan manyan cibiyoyi biyu ba za a taba mayar da su gefe ba, domin kuwa su ne gishikin dukkanin ilmomin mazhabar iyalan gidan manzo a wannan zamani.
441564