Kamfanin dillancin labaran Ikna ya nakalto daga kamfanin dillancin labaran sana na kasar Syria cewa; Babban daraktan kungiyar hadin kan kasashen musulmi ta OIC Ihsan Ikmal Auglo ya yi kakkausar suka dangane da yadda Isra'ila take ci gaba da danne hakkokin palastinawa a birnin Qods mai alfarma. Bayanin ya ci gaba da cewa yahudawan sahyuniya suna barazanar rushe masallacin Qods wannan ne ya sanya shugaban kwamitin kula da harkokin masallacin qods din Ikrama sabri ya kirayi dukkanin palastinawa mazauna birnin Qods da su taru a masallacin a ranakun litinin da talata, domin hakan yana firgita yahudawa.442616