Kamfanin dillancin labaran Ikna ya nakalto daga bangaren yada labarai na cibiyar kula da harkokin wasan kwaikwayo ta Iran cewa; Za a gudanar da wani babban taro kan wasannan kwaikwayo a mahangar addinin muslunci da kuma rawar da yake takawa wajen wayar da kan mabiya addinin musulunci a dukkanin sassa na duniya. Ya ci gaba da cewa abin koyi ne ga dukkanin muslmin duniya da su kalli yadda al'ummar Iran suke yin riko da kur'ani, wanda kuma hakan ne ya bas u izza a duniya baki daya, wanda hakan ke nuni da cewa riko da kur'ani na tattare da samun izza.
442755