IQNA

An Fara Gasar Kasa Da Kasa Ta Alkur'ani A Aljazira

16:45 - September 12, 2009
Lambar Labari: 1825181
Bangaren kasa da kasa: an fara gasar karatun kur'ani ta kasa da kasa a kasar Aljeriya karo na shidda tare da tafsirin kur'ani.
Cibiyar da ke kula da harkokin kur'ani a Iran Ikna ce bayan ta nakalto daga jaridar Bilad ta kasar Aljeriya ta watsa rahoton dake tabbatar da fara gasar karatun kur'ani da tafsiri ta kasa da kasa karo na shidda kuma an samu halartar shugaban wannan kasa ta Aljeriya Abdul Aziz Butafilika kuma za a share mako guda ana tabka wannan gasa da aka samu halartar makaranta da masu tafsiri daga kasashe bakwai na duniya .kuma ministan da ke kula da harkokin addini a kasar ne ya shaida haka.

463406


captcha