Bangaren kasa da kasa; An fara gudanar gasar karatu kur'ani ta kasa da kasa a karo na shida a kasar Kuwait, wadda ke samun halartar mahardata da makaranta kur'ani mai tsarki daga kasashen musulmi daban-daban.
Kamfanin dillancin labaran Iqna ya nakalto daga jaridar kasar kuwait ta Albilad cewa; An fara gudanar gasar karatu kur'ani ta kasa da kasa a karo na shida a kasar kuwai, wadda ke samun halartar mahardata da makaranta kur'ani mai tsarki daga kasashen musulmi daban-daban. Bayanin ya ci gaba da cewa wannan gasa ita ce karo na shida da aka fara gudanar da ita , wadda aka bude tare da halartar manyan jami'an gwamnatin kasar da suka hada da shi kansa shugaban kasar. Za a kwashe kimanin mako guda ana gudanar da wannan gasar karatun kur'ani a kasar. 463319