IQNA

Kur'ani Mai Tsarki Na Tattare Da Manya Mu'ujizozi Ga Dan Adam

8:46 - September 14, 2009
Lambar Labari: 1825801
Bangaren kasa da kasa; Bangaren gudanar da bincike n jami'ar kasa da kasa da ke kasar Jamus ya gano cewa kur'ani yana tattare da wasu lamurra wadanda suka gajiyar dad an adam wato mu'ujiza.
Kamfanin dillancin labaran iqna ya nakalto daga wasu kafofin yada labarai na kasar Jamus cewa, Bangaren gudanar da bincike n jami'ar kasa da kasa da ke kasar Jamus ya gano cewa kur'ani yana tattare da wasu lamurra wadanda suka gajiyar dad an adam wato mu'ujiza, dad an adam bai taba shedawa a tarihinsa ba. Bayanin ya ci gaba da cewa masu binciken sun mayar da hankali ne kan tarihin kur'ani da kuma kwatanta shekarun safkar da shi, da kuma yadda ya kunshi ilmomin da suka gabata dubban shekaru da suka gabata, tare da bayyana wasu ababe da suka biyo bayan safkarsa da shekaru daruruwa ko sama da dubu daya, wanda hakan ke tabbatar da cewa kur'ani ya gajyar dad an adam ta fuskoki da dama, musamman ma ta fuskar ilimi. 463869

captcha