Kamfanin dillancin labaran Iqna ya nakalto daga shafin internet na islam online cewa; Musulmin kasar Australia sun bukaci gwamnatin kasar da ta ba su hutu a ranakun idin Musulunci, ta yadda ba za su yi aiki ba a hukumance. Bayanin ya ci gaba da cewa bisa la'akari da yawan da musulmi suke d shi a kasar Australia, ya sanya suna fuskantar matsaloli na rashin samun 'yancin gudanar da bukukuwansu na Musulunci kamar yadda suke so, wannan ya sanya suka bukaci gwamnatin kasar da ta amince ta bayar da dama ga musulmi da su rika daukar hutu a ranakun idi a hukumnce. 463974