Bangaren kasa da kasa; Shugaban cibiyar kula da al'adun musulunci ta Iran ya bayyana cewa babbar manufar azumi ita ce tarbiyantar da rai tare da kusantar da shi zuwa ga Allah madaukakain sarki, tare da samun takawa.
Kamfanin dillancin labaran Iqna ya habarta cewa a wani zaman buda baki da aka gudanar jiya, wanda ya samu halartar manyan jami'an gwamnatin Iran a birnin Teharan, an gudanar da bayanai kan manufar azumi dav kuma amfaninsa ga mutum, a yayin gudanar da taron, Shugaban cibiyar kula da al'adun musulunci ta Iran ya bayyana cewa babbar manufar azumi ita ce tarbiyantar da rai tare da kusantar da shi zuwa ga Allah madaukakain sarki, tare da samun takawa.464516