Bangaren kur'ani; An gudanar da sallar juma'a ta karshen watan Ramadan a birnin Moscow na kasar Rasha, inda aka gabatar da bayanai dangane da ranar Qods, wanda ya samu halartar dubban musulmin birnin.
Kamfanin dillancin labaran iqna ya nakalto daga bangaen yada labaransa na na birnin Moscow cewa; An gudanar da sallar juma'a ta karshen watan Ramadan a birnin Moscow na kasar Rasha, inda aka gabatar da bayanai dangane da ranar Qods, wanda ya samu halartar dubban musulmin birnin. Bayanin ya ci gaba da cewa wannan taro ya samu karbuwa wajen dubban musulmin birnin, inda suka kara fahimtar muhimmancin masallacin Qods a wurin al'ummar musulmi. 466961