Bangaren siyasa; Shugaban kasar Iran Mahmud Ahmadinejad ya bayyana cewa za a iya samun sulhu da zaman lafiya ne kawai a duniya ta hanyar girmama juna tsakanin al'ummomin duniya da gwamnatocin kasashe,
Kamfanin dillancin labaran Iqna ya nakalto daga shafin internet na bangaren yada labarai na ofishin shugaban kasar Iran Mahmud Ahadinejad cewa; a lokacin yake barin birnin Tehran domin kama hanya zuwa birnin New York na kasar Amurka, shugaban kasar Iran din ya bayyana cewa; za a iya samun sulhu da zaman lafiya ne kawai a duniya ta hanyar girmama juna tsakanin al'ummomin duniya da gwamnatocin kasashe, ba tahanyar barazana da mayar da wasu saniyar ware ba.468259