Kamfanin dillancin labaran iqna ya nakalto daga kamfanin dillancin labaran turkrus cewa; An fara gudanar da zaman taro tsakanin gwamnatin Rasha da kuma kasashen musulmi, wanda aka fara jiya a birnin Moscow fadar mulkin kasar. An bude zaman taron ne da karanta bayanin shugaban kasar rasha Dmitry Medvedev, sai kuma bayanin babban sakataren kungiyar hadin kan kasashen musulmi Ihsan Oglo. Bayanin ya ci gaba da cewa babbar manuufar gudanar da wannan zaman taro ita ce kara kusanto da fahimta tsakanin bangarorin biyu, ta yadda za su ci gaba da gudanar da aiki kafada da kafada domin amfanar juna. 469276