IQNA

Musulmin Rasha Na Karfafa Dangantakar Kasar Da Kasashen Musulmi

16:47 - September 26, 2009
Lambar Labari: 1830115
Bangaren kasa da kasa; A lokacin da yake gabatar da jawabin bude taron hadin gwiwa tsakanin gwamnatin Rasha da duniyar musulmi, Alexender Torshen ya bayyana cewa musulmin Rasha su ne igiyar daura kyakkyawar dangantaka tsakanin Rasha da sauran kasashen musulmi.
Kamfanin dillancin labaran Iqna ya nakalto daga shafin internet na kamfanin dillancin labaran Rusia alyaum cewa; A lokacin da yake gabatar da jawabin bude taron hadin gwiwa tsakanin gwamnatin Rasha da duniyar musulmi, Alexender Torshen ya bayyana cewa musulmin Rasha su ne igiyar daura kyakkyawar dangantaka tsakanin Rasha da sauran kasashen musulmi. Bayanin ya ci gaba da cewa An bude zaman taron ne da karanta bayanin shugaban kasar rasha Dmitry Medvedev, sai kuma bayanin babban sakataren kungiyar hadin kan kasashen musulmi Ihsan Oglo. Bayanin ya ksrs da cewa babbar manuufar gudanar da wannan zaman taro ita ce kara kusanto da fahimta tsakanin bangarorin biyu, ta yadda za su ci gaba da gudanar da aiki kafada da kafada domin amfanar juna. 469323


captcha