Kamfanin dillancin labaran Iqna ya nakalto daga kamfanin dillancin labaran lavieeco cewa; Za a gudanar da wani zaman taro na kasa da kasa a birnin Ribat na kasar Morocco dangane da ma'anar kyawawan dabi'u na musulunci da ya kamatasa su koya domin kyuatata rayuwarsu mai makon koyi da dabi'un turai. Bayanin ya ci gaba da cewa taron zai samu halartar masana daga kasashen musulmi daban-daban. Taron dai zai mayar da hankali kan bahasi dangane da abin day a kamata matasa musulmi su yi riko da shi na gyara dabi'unsu. 469324