Kamfanin dillancin labaran Iqna ya nakalto daga shafin internet na kungiyar kula da harkokin ilimi da al'adu na kasahen musulmi ISESCO cewa; Za a gudanar da wani zama na ministocin harkokin al'adu na kasashen musulmi a birnin Baku na kasar Azarbaijan a makonni uku masu zuwa. Bayanin ya ci gaba da cewa wannan taro zai samu halartar ministocin ne daga kasashen musulmi, domin yin dubi kan muhimman batutuwa da suka danganci al'du na Musulunci, kuma wannan shi ne karo na shida da ake gudanar da irin wannan taro. 469520