Bangaren kasa da kasa; An sake buga ittafin na mu'jizozin kura'ni mai tsarki a kasar Masar, wanda ya kawo muhimman batutuwa suka shafi mu'ijiza a cikin kur'ani, wanda malamamin nan Atif Maliji.
Kamfanin dillancin labaran Iqna ya nakalto daga shafin internet na kamfanin dillancin labaran Yaum Sabe cewa; An sake buga ittafin na mu'jizozin kura'ni mai tsarki a kasar Masar, wanda ya kawo muhimman batutuwa suka shafi mu'ijiza a cikin kur'ani, wanda malamamin nan Atif Maliji. Bayanin ya ci gaba da cewa wannan littafi ya samu karbuwa daga musulmin kasar masar da ma sauran musulmi na duniya, domin kuwa wannan shi ne karo na biyar da aka sake buga shi bayan da dukkanin wadanda aka buga a lokutan bayasuka kare, ta yadda babu shi a kasuwa. 469650