IQNA

Gwamnatin Sweden Ba Ta Yi Lale Marhabin Da Ziyarar Liberman Ba

14:27 - September 27, 2009
Lambar Labari: 1830547
Bangaren kasa da kasa; Ministan harkokin wajen kasar Sweden ya ki amincewa ya gana da ministan harkokin wajen Haramtacciyar kasar Isra'ila Liberman.
Kamfanin dillancin labaran Iqna ya nakalto daga kamfanin dillancin labaran Palstine info cewa; Ministan harkokin wajen kasar Sweden ya ki amincewa ya gana da ministan harkokin wajen Haramtacciyar kasar Isra'ila Liberman. Ministan na kasar Sweden ya ki amincewa ya gana da ministan harkokin haramtacciyar gwamnatin yahudawan ne sakamakon sace bangarorin jikin palastinawa da suka kashe ne suna sayarwa kasashen yammacin turai, wanda gwamnatin Sweden take kallon hakan a matsayin wani mummunan aiki. 469669
captcha