IQNA

Za A Gudanar Da Tarukan Kasa Da Kasa Kan ilmomin Musulunci A Rasha

14:27 - September 27, 2009
Lambar Labari: 1830549
Bangaren kasa da kasa; Za a gudanar da tarukan kasa da kasa dangane da ilmomin addinin Musulunci a jami'oin Musulunci da ke cikin yankunan Rasha da kewaye, wanda za a fara gudanarwa daga mako mai kamawa.
Kamfanin dillancin labaran iqna ya nakalto daga shafin internet na ISESCO cewa; Za a gudanar da tarukan kasa da kasa dangane da ilmomin addinin Musulunci a jami'oin Musulunci da ke cikin yankunan Rasha da kewaye, wanda za a fara gudanarwa daga mako mai kamawa. Bayanin ya ci gaba da cewa wannan taro zai samu halartar masana daga sassa daban-daban na kasashen musulmi da kuma masana daga wasu kasashen musamman ma na yankunan Rasha, taron zai mayar da hankali ne kan yadda ya kamata a rika yin amfani da koyarwar Musulunci a cikin zamantakewar musulmi mazauna yankunan Rasha da kewaye. 469776


captcha