IQNA

Bincike Kan Halin Palasdinawa A Ganawar Shugaban Iran Da MDD

18:59 - September 27, 2009
Lambar Labari: 1830629
Bangaren siyasa : shugaban kasar Iran a lokacin ganawarsa da shugaban Majalisar dinkin duniya sun tabo matsalolin da ke addabar Palasdinawa da halin da suke ciki a yau.
Cibiyar da ke kula da harkokin kur'ani a Iran Ikna ce ta watsa rahoton cewa; ta nakalto daga majiyar fadar shugaban kasar Iran Ahmadi najad cewa lokacin ganawarsa da babban sakataren majalisar dinkin duniya sun tabo halin da palasdinawa ke ciki a yau da kumcin da gwamnatin haramtacciyar kasar Isra'ila ta sanya su a ciki tare da tunanin hanyoyin kawo karshen halin da suke ciki da kuma yankin gabas ta tsakiya baki daya. Wannan ganawa dai ta z one a daidai lokacin gudanar da babban taron majalisar dinkin duniya da aka gudanar a birnin Newyork na kasar Amerika.

469810
captcha