IQNA

A Yau Ne Aka Cika Shekara Guda Da Rushe Wani Bangare Na Makabartar Baki'a

14:30 - September 28, 2009
Lambar Labari: 1831048
Bangaren kasa da kasa; A yau muslmi mabiya mazhabar ahlul bait a kasar saudiyya suke gudanar da tarukan cika shekara guda da gwamnatin wahabiyawan saudiyya ta rushe wani bangare na makabartar baki'a.
Kamfanin dillancin labaran Iqna ya nakalto daga tashar talabijin ta Rasid cewa; A yau muslmi mabiya mazhabar ahlul bait a kasar saudiyya suke gudanar da tarukan cika shekara guda da gwamnatin wahabiyawan saudiyya ta rushe wani bangare na makabartar baki'a. Bayanin ya ci gaba da wahabiyan saudiyya sun kai farmaki musulmi da suke gudanar da ziyara a kabrukan ahlul bait da sahabban manzon Allah da ke makabartar baki'a a madina a shekarar da ta gabata, inda a yau aka cika shekara guda aikata wannan mummunan aiki. 470356



captcha